Babin Zababbu Daga Hikimomin Amirul Muminina (A.S) Da Wa’azozinsa, Ya Hada Da Amsoshin Tambayoyinsa Da Gajerun Kalamansa Da Makamantansu.

1.  Ka zama cikin fitina kamar dan saniya mai shan nono bashi da baya balle a hau kuma bashi da hantsa balle a tatsa.

2.  Wanda ya yi kwadayi ya wulakanta kansa, wanda ya bayyanar da matsalarsa (asirinsa) ya yarda da kaskanci, wanda ya sallada harshensa (ya saki harshensa) akan ransa ya wulakanta ta, rowa aibi ne, tsoro tawaya ne, talauci yana dakusar da kaifin hankali gabarin hujjarsa, mai karantawa bako ne a garin sa, gajiyawa aibi ne, dauriya jarunta ne, zuhudu jari ne, taka tsantsan garkuwa ne, madalla da aboki (ya zama) yarda, ilmi gado ne mai daraja, ladabi ado ne mai sabuntuwa, tunani karau ne mai tsafta, kirjin mai hankali akwatin sirrinsa, sakin fuska tarkon soyayya ne, kawo hanzari kabarin aibobi ne.

3.  Amincewa juna maboyar aibi ne, duk wanda ya amincewa kansa fushi zai karu a kansa, sadaka magani ce mai warkarwa, ayyukan bayi na ibada a magaggauciya [Duniya] natsuwar (farin cikin) ido ne a majinkirciya [Lahira]

4.   Abin mamaki ga mutum yana gani ta hanyar kitse, yana Magana ta hanyar tsoka, yana ji ta hanyar kashi, kuma yana numfashi ta hanyar kafa.

5.   Idan duniya ta fuskanto mutum sai ta ara masa kyawawan waninsa, amma idan ta bada baya gare shi sai ta kwace masa kyawawan kansa.

6.   Kuyi ma’amala da mutane irin mu’amalar da in kun rasu zasu yi kukan rashinku, sannan  in kun rayu zasu kaunace ku.

7.   Idan ka sami iko akan makiyin ka, to ka sanya afuwa gare shi ta zama godiya ga Allah akan wannan iko da ka samu a kansa.

8.   Mafi gajiyawar mutane wanda ya kasa samun yardar ‘yanuwa, mafi gajiyawa daga gareshi shi ne wanda ya tozarta wanda ya samu daga cikinsu.

9.   Idan farkon ni’imomi suka zo muku, to kada ko kore mafi nisanta da karancin godiya.

10.   Wanda na kusa ya tozarta shi, sai a yalwata masa samun na nesa.

11.   Ba duk wanda aka fitanar ba ne abin zargi.

12.   Abubuwa suna rusunawa gaddarawa, har sai ajali ya yi halinsa.

13.   An tambaye shi game da fadin annabi (S.A.W) “ku canja furfura, kada ku yi kama da yahudawa”. Sai ya ce manzo ya fadi haka ne a lokacin da addini ya karanta (musulmi ba su da yawa) amma yanzu addini ya fadada, ya kuma karfafa, kowa yana iya yin abinda ya zaba.

14.   Ya fada game da wadanda suka ki yaki tare da shi: sun bar gaskiya, ba su taimaki barna ba.

15.   Wanda ya yi tafiya a tsakatsakin burinsa, ya hadu da ajalinsa.

16.   Ku zode wa ma’abota mutunci kananan laifuffukansu, domin ba wanda zai yi kuskure daga cikinsu sai hannunsa ya kasance a hannun Allah yana daukaka shi.

17.   An gwama tsorata da rasawa (idan ka ji tsoron yin abu ka rasa shi), kunya kuma da hani (haka nan wanda ya faye jin kunyar abu sai ya rasa), dama tana wucewa ne kamar wucewar gajimare, ku riki damar alheri.

18.   Muna da hakki idan an ba mu shi, in ba haka ba (ba a ba mu ba) sai mu hau kan duwainiyar rakumi, (wato sai mu dau hakuri) komai daren dadewa. Hawa duwainiyar rakumi gun larabawa alama ce ta kaskantar da mai hakki, wato wanda aka goya a baya rakumi yana zama dai dai kan duwainiyarsa ne ba gaba ba, wato kamar yaro ko bawa da ake goyawa a bayan rakumi ne[1].

19.   Wanda aikinsa ya jinkirtar da shi, dangantakarsa ba zata daukaka shi ba.

20.   Yana daga kaffarar zunubai taimakon wanda yake cikin kunci, da yaye wa mai bakin ciki bakin cikinsa.

21.   Ya kai dan adam, idan ka ga ubangijinka yana bibiyar ni’imarsa a gareka kana saba masa, to ka kiyaye shi.

22.   Ba wanda ya taba boye wani abu sai ya bayyana a harshensa da fadin fuskarsa.

23.   Tafi tare da ciwonka matukar zai tafiyu tare da kai. (Amma idan ba zaka iya ci gaba da aiki ba sai ka huta)

24.   Mafificin zuhudu, shi ne boye zuhudu.

25.   Idan ka kasance cikin tahowa da-baya-da-baya, mutuwa kuma cikin gabatowa gaba, to lallai ya mamakin saurin haduwa!

26.   Hattara hattara! Na rantse da Allah ubangiji ya boye (kurakurai) kai ka ce ya riga ya gafarta.

27.   An tambaye shi game da imani sai ya ce yana kai ginshiakai hudu ne: akan juriya, da yakini, da adalci, da jihadi: Hakuri yana kan rassa hudu: akan shauki, da tsoro, da zuhudu, da taka-tsantsan: wanda ya so aljanna zai fidiye daga shahawaice-shahawaice, wanda ya ji tsoron wuta zai nisanci haram, wanda ya yi gudun duniya zai ga saukin musibu, wanda ya yi sauraron mutuwa zai gaggauta zuwa aikata alherai.

Yakini yana kan rassa hudu ne: akan kaifin kwakwalwa, da fassarar hikima, da wa’aztuwa da daukan darasi, da bin dabi’un magabata: wanda ya ke da kwakwalwa hikima zata bayyana gareshi, wanda hikima ta bayyana gareshi zai dau darasi, wanda ya dau darasi, kamar yana cikin na farko ne.

Adalci yana kan rassa hudu ne: akan zufin fahimta, da sirrin ilimi, da kayen ni’ima, da kafaffen hakuri: duk wanda ya fahimata zai san zurfafan ilimi, wanda ya san zurfafan ilimi zai zo da komai daga hukunce-hukunce, wanda ya yi hakuri ba zai yi shisshigi da wuce gona da iri a al’amuransa ba, kuma zai rayu cikin mutane abin yabo.

Jihadi kuma Yana Kan rassa hudu ne: Akan umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna, da gaskiya a ko’ina, da kin fasikai. Wanda ya yi umarni da kyakkyawa ya karfafi muminai, Wanda ya hana mummuna ya turmuza hancin munafukai a kasa (ya bakanta ran munafikai), Wanda ya yi gaskiya a ko’ina ya sauke nauyin da yake Kansa, Wanda ya ki fasikai ya yi fushi saboda Allah Allah zai yi fushi saboda shi ya kuma yardar da shi ranar sakamako.

Kafirci yana kan shika-shikai hudu ne: akan zurfafawa, da jayayya, da karkata, da sabawa: wanda ya zurfafa ba zai karkata zuwa ga gaskiya ba, wanda jayayyarsa ta yi yawa da jahilci makantarsa ga barin gaskiya zata dawwama, wanda ya karakace mummuna zai zama kyakkyawa gunsa kuma kyakkyawa ya zama mummuna gunsa ya yi maye mayen bata, wanda ya saba hanyoyinsa zasu kulle masa (su yi tsauri), al’amarinsa ya tsananta, mafitarsa ta yi wahala ta kuntata.

 Kokwanto yana kan rassa hudu ne: akan jayayya, da tsoro, da kai-kawo, da mika wuya: wanda ya sanya jayayya ta zama masa al’ada darensa ba zai waye ba, wanda abinda yake gabansa ya tsorata shi zai sallama (tankwasa ya rusuna akan kafafunsa) a gabansa, wanda ya kai-kawo a kokwanto kofatun shedanu sa tattaka shi, wanda ya mika wuya ga halakar duniya da lahira zai halaka a cikinsu.

28. Mai aikata alheri ya fi alheri alheri, mai aikata sharri ya fi sharri sharri. (wato mai aikata alheri shi ne mafi girman alheri daga alheri shi kansa, haka ma mai sharri shi  ya fi sharri zama sharri)

29. Ka zama mai sauki kada ka zama mai almubazzaranci, ka zama mai tsakaitawa, kada ka zama mai kwauro.

30. Mafi girman wadata barin buri.

31. Wanda ya gaggautawa mutane (wato farkon saninsu da shi) da abinda suke ki, sai su fadi abinda ba su sani ba game da shi.

32. Wanda ya tsawaita buri zai munana aiki.

33. Dagatoci sun hadu da shi akan hanyarsa ta sham sai suka sauka daga kan dawakansu suka gaggauta  zuwa wajansa:

Sai ya ce da su: menene wannan kuka aikata? 

Sai suka ce: dabi’a ce da muke girmama sarakunanmu da ita.

Sai (A.S) ya ce: wallahi wannan ba zai amfana wa sarakunanku komai ba, ku kuna tsanantawa kanku ne kawai a duniya ku kuma tabe da shi a lahira, tir da wahala da bayanta azaba ce, kuma ribar sakin fuska ta yawaita da aminci daga wuta yake tare da ita.

34. Yana mai gaya wa dansa Hasan (A.S): ya kai dana ka kiyaye hudu daga gareni, matukar ka yi aiki da su ba abinda zai cutar da kai: Hakika mafi wadatar wadata shi ne hankali, mafi girman talauci shi ne wauta, mafi dimuwar dimuwa shi ne ji-ji-da-kai, mafi girman nasaba shi ne kyawun dabi’u.

Ya dana na hana ka abota da wawa, domin shi ya kan so ya amfane ka sai ya cutar da kai. Kuma na hana ka abota da marowaci, domin shi ya barka shi ne ya fi da bukatuwar da zaka zama kana yi masa.

Na hanaka abota da fajiri, domin shi zai iya sayar da kai da dan kankanin abu. Na hana ka abota da makaryaci, domin shi kamar sururi ne: da yake kusantar da nesa gareka, yake nesantar da kusa gabarinka.

35. Babu wani kusanci da Allah da nafiloli, idan ta cutar da farillai.

36. Harshen mai hankali yana bayan zuciyarsa, zuciyar wawa tana bayan harshensa[2].

Wata ruwayar tana cewa zuciyar wawa tana bakinsa, harshen mai hankali yana zuciyarsa. (Ma’anarsu da ta sama daya ce).

37. Yana mai gaya wa wani daga sahabbansa da ya samu wata rashin lafiya: Allah ya sanya zoginka ya zama shafewa ga zunubanka, domin rashin lafiya ba shi da lada sai dai yana shafe zunubai, yana kakkabe ta irin kakkabewar ganyayyakin itace, domin lada kadai yana samuwa ne ta hanyar zance da harshe, da aiki da hannaye da kafafu, kuma Allah yana shigar da wanda ya so daga bayinsa aljanna da kyakkyawar niyya da zuciya ta gari.

38. Game da Habbab Dan Aratt yana cewa: Allah ya ji kan Habbab, ya musulunta da son kansa, ya yi hijira yana mai biyayya, ya wadatu da kadan, ya yarda da ubangijinsa, ya rayu mai jihadi.

39. Farin ciki ya tabbata ga Wanda ya tuna lahira, ya yi aiki saboda hisabi, ya wadatu da kadan, ya yarda da hukuncin ubangijinsa.

40. Da zan doki hancin mumini da takobina wannan akan sai ya ki ni da bai ki ni ba, da na zuba duniya da dukkan kawanyarta (adonta) ga munafuki akan sai ya so ni da bai so ni ba: saboda an hukunta kuma ya zartu daga harshen Annabi ummiyyi (S.A.W) cewa: “Ya Ali! Mumini ba zai ki ba, munafuki ba zai so ka ba”.

41. Mummuna da zai bata maka rai shi ya fi kyakkyawa da take kayatar da kai a wajan Allah.

42. Kimar mutum tana daidai gwargwadon himmarsa, gaskiyarsa kuma tana daidai mutuncinsa, jarumtakarsa tana daidai gwargwadon karfinsa, kamewarsa tana daidai gwargwadon kishinsa.

43. Rabauta da daukar niyya ne, niyya kuma tana daga tuntuntunin ra’ayi, ra’ayi kuma yana samuwa da kewaye sirrai.

 (Matakai ne guda hudu akwai ilimi da abu da sanin sirrinsa, sannan sai kyakkyawan ra’ayi, sannan niyya da azama akansa sannan sai a shiga aikata shi a samu rabauta).

44. Ku ji tsoron hayewar mai karimci idan ya ji yunwa, marowaci kuma idan ya koshi.

45. Zukatan maza dabbar daji ce, wanda ya saba da ita sai ta kusanto gareshi.

46. Ka rabauta kwarai matukar aibinka ya zama asirtacce.

47. Wanda ya fi cancanta a cikin mutane ya yi afuwa shi ne wanda ya fi ikon ukuba daga cikinsu.

48. Kyauta ita ce wacce take tun farko, amma idan ta kasance domin an roka ne to wannan kunya ce da gudun zargi.

49. Babu wadata kamar hankali, babu talauci kamar jahilci, babu gado kamar ladabi, babu mai taimako kamar shawara.

50. Hakuri kala biyu ne: hakuri akan abin da kake ki, da hakuri gabarin abinda kake so.

51. Wadata acikin bakunta zaman gari ne, talauci a cikin zaman gari bakunta ce.

52. Wadata dukiya ce da ba ta karewa.

53. Dukiya mabubbugar shahawa ce.

54. Wanda ya yi maka gargadi kamar wanda ya yi maka albishir ne.

55. Harshe zaki ne, idan aka bar shi sai ya yi cizo.

56. Mace kunama ce harbinta mai zaki ne.

57. Idan aka gaishe da kai da gaisuwa to ka amsa da mafi kyawunta, idan aka mika maka hannu ka saka mata da abin da ya zarta nata, amma duk da haka fifiko yana ga wanda ya fara.

58. Mai ceto shi ne ginshikin (karfin) mai nema.

59. Mutanen duniya kamar matafiya ne da ake tafiya da su alhalin suna bacci.

60. Rashin masoya bakunta ne.

61. Kubucewar bukata ya fi sauki daga nemanta wajan wadanda ba ma’abotanta ba.

62. Kada ka ji kunyar bayar da kadan domin hanawa ya fi shi karanci.

63. Kamewa (gabarin tambaya) adon talauci ne, godiya adon wadata ce.

64. Idan babu abinda kake nema (ko kuma abin da kake so bai wakana ba) to kada ka damu da yaya ka kasance.

65. Ba yadda zaka ga jahili sai dai imma mai wuce gona da iri ko mai gazawa.

66. Idan hankali ya cika Magana sai ta yi karanci.

67. Zamani yana tsofar da jiki, yana kuma jaddada buri, yana kusantar da mutuwa, yana nesantar da burace-burace, wanda ya same shi ya jigata, wanda ya kubuce masa ya wahala.

68. Wanda ya sanya Kansa shugaba ga mutane to yana kansa ya fara koyar da kansa kafin ya koyar da waninsa, ya zama tarbiyyatar da zuciya kafin ya tarbiyyatar da harshensa, mai koyar da kansa mai ladabtar da ita shi ya fi cancanta da girmamawa fiye da mai koyar da mutane mai ladabtar da su.

69- Lumfashin mutum takunsa ne zuwa ajalins.

70- Duk abin kididdiga mai tawaya ne, kuma duk abin da ake sauraro mai zuwa ne.

71- Idan al'amura suka rikitar suke cakude sai a kiyasta karshenta da farkonta.

72- Daga labarin Dhirar dan Dhamuratad Dhubabi yayin da ya shiga wajan Mu'awiya da kuma tambayarsa game da Amirulmunin (A.S) ya ce: Na shaida hakika na gan shi a irin tsayuwar da yake yi dare ya riga ya yi duhu, yana mai tsayuwa a mihrabinsa yana rike da gemunsa yana mai makyarkyata irin makyarkyatar wanda aka sara[3], yana mai kuka kukan mai bakin ciki, yana cewa: Ya duniya! Ya duniya! Ki yi nesa da ni, shin kin zo mini ne ko kuma kina shauki da bege zuwa gareni? A'aha, Ki sani lokacin da zaki shiga zuciyata bai yi ba tukuna! Ya munana har abada! Ki yaudari wanina, ba na bukatar ki, hakika na riga na sake ki saki uku da babu dawowa a cikinta!

Rayuwarki gajeriya ce, al'amarinki kankani ne, burinki wulakantacce ne.

Wayyo! Saboda karancin guzuri, da tsayin tafarki, da nisan tafiya, da girman mashiga!

73- Yana daga cikin maganarsa yayinda mai tambaya ya tambaye shi: Shin tafiyar mu zuwa Sham da hukuncin Allah ne da kuma kaddarawarsa? Bayan magana mai tsayi yana mai cewa: Kaiconka! Kai kana tsammanin hukunci na tilas, da kuma kaddara ta lallai! Da kuma ya kasance haka ne da lada da azaba sun zama wasa, da kuma alkawari da narko sun saraya.

Allah madaukakin sarki ya umarci bayinsa bisa zabi, ya hana su bisa tsoratarwa, ya kuma kallafa musu mai sauki, bai kallafa musu mai tsanani ba, ya ba su mai yawa a kan dan kadan –da suka aikata- ba a kuma saba masa don rinjayarsa, ba a bi shi don tilastawa ba, bai kuma aiko annabawa don wasa ba, bai saukar da littafi don raha ba, bai kuma halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu don barna ba, “Wannan shi ne tsammanin wadanda suka kafirta, to azabar wuta ta tabbata a kan wadanda suka kafita”

74. Imam Ali (A.S) ya ce:  ka karbi hikima ko’ina take, ka sani hikima tana kasancewa a kirjin munafuki sai ta jujjuya a kirjinsa har sai ta fita sai ta zauna tana mai tafiya zuwa ga ma’abotanta a cikin kirjin mumini.

75. Imam Ali (A.S) ya fadi kwatankwacin hakan: Hikima bataccen kayan mumini ne, ka riki (karbi) hikima koda kuwa daga munafukai ne.

76. Imam Ali (A.S) ya ce: Kimar kowane mutum shi ne abin da yake kayatar da shi.

{wasu sun fassara wannan magana da cewa “Kimar kowane mutum shi ne abin da yake kawatuwa da shi” ko kuma “Kimar kowane mutum (wato; abin da yake ba wa mutum kima) shi ne abin da mutum din yake kyautata shi”}

77. Imam Ali (A.S) ya ce: na yi muku wasici da abubuwa biyar da zaku yi tafiye-tafiye da rakuma domin ku same su da sun cancanci hakan: kada wani daga cikinku ya kaunaci kowa sai ubangijinsa, kuma kada ya ji tsoro sai zunubansa, kada wani ya ji kunya idan aka tambaye shi abin da bai sani ba ya ce: ban sani ba, kuma kada wani ya ji kunya idan bai san wani abu ba ya nemi saninsa.

Kuma game da hakuri, hakika misalin hakuri ga imani kamar misalin kai ne ga jiki, kuma babu wani alheri ga jikin dab a shi da kai, ko kuma imanin dab a shi da hakuri tare da shi.

78. Imam Ali (A.S) ya ce da wani mutum da ya yawaita yabonsa, kuma alhalin Imam (A.S) ya kasance yana sanin cewa (shi wannan mutumin karya yake yi a zuciyarsa): Ni ina kasan abin da ka fada, kuma sama da abin da yake cikin ranka nake.

79. Imam Ali (A.S) ya ce: ragowar takobi (mutanen da suka rage bayan yaki domin ‘yancinsu) su ne wadanda jama’arsu ta fi wanzuwa, kuma suka fi  yawaitar yaduwar ‘ya’ya.

80. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya bar fadin: ban sani ba, to an samu makasarsa.

81. Imam Ali (A.S) ya ce: ra’ayin dattijo ya fi soyuwa gareni fiye da karfin jarumtakar saurayi.

An ruwaito a wata ruwaya fiye da halartar saurayi (a wajen yaki).

82. Imam Ali (A.S) ya ce: Ina mamakin wanda yake yanke kauna alhalin akwai istigfari tare da shi.

  

83. Abu Ja’afar Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ruwaito daga Imam Ali (A.S) ya ce: Akwai aminci biyu masu tseratarwa daga azabar Allah (S.W.T) da suka kasance a fadin kasa, gashi hakika an riga an dauke dayan, don haka ku yi riko da dayan: amma wanda aka dauke shi ne manzon Allah (S.A.W).

Amma wanda ya wanzu shi ne istigfari, ubangiji madaukaki ya ce: “Allah bai kasance mai yi musu azaba ba alhalin kai kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai yi musu azaba ba alhalin suna istigfari”.

84. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya gyara tsakaninsa da Allah to Allah zai gyara tsakaninsa da mutane, wanda kuma ya gyara lahirarsa, to Allah zai gyara masa duniyarsa, wanda kuma ya kasance mai yi wa kansa wa’azi, to Allah zai kasance mai kiyaye wa gareshi.

85. Imam Ali (A.S) ya ce: malamin da lallai shi ne ya isa malami shi ne wanda bai sanya mutane sun yanke kauna daga rahamar Allah ba, kuma bai sanya su yanke kauna daga tausayawar Allah ba, kuma bai amintar da su daga makircin (azabar) Allah ba.

86. Imam Ali (A.S) ya ce: mafi kaskancin ilimi shi ne wanda ya tsaya a kan harshe kawai, mafi daukakarsa shi ne wanda ya bayyana a kan gabobi da sassan asali na jiki.

  

87. Imam Ali (A.S) ya ce: Hakika wadannan zukata suna kosawa kamar yadda jikunkuna suke kosawa, don haka ku nema mata hikima mai dadi.

88.Imam Ali (A.S): kada xayanuk Ya ce: ya ubangiji ni ina neman tsarinka daga fitina, domin babu wani mutum sai yana tare da wata fitina, sai dai dukkan wanda zai nemi tsari to ya nemi tsari daga masu vatarwa na daga fitinu, haqiqa Allah maxaukaki yana cewa: “Ku sani cewa haqiqa dukiyoyinku ‘ya’yanku fitina ne”, ma’anar wannan shi ne; cewa shi maxaukaki yana jarraba su da dukiyoyi da ‘ya’ya domin ya bayyanar da mai fushi da arzikinsa da kuma wanda ya yarda da rabonsa, duk da kuwa ubangiji maxaukaki ya fi su sanin kawukansu, sai dai domin ya bayyanar da ayyukan da, da sun e zasu cancanci lada da uquba, domin wasu suna son maza kuma suna qin mata, wasu kuma suna son juya (havaka) dukiya ne suna qin tawayar halal.

Wannan yana daga cikin maganganu masu qayatarwa da aka ji daga gareshi (A.S) a tafsiri.

89. An tambayi Imam Ali (A.S) game da alheri mene ne shi? Sai Imam Ali (A.S) ya ce: alheri ba shi ne dukiyarka da ‘ya’yanka su yawaita ba, sai dai alheri shi ne; iliminka ya yawaita, kuma haqurinka ya girmama, kuma ka yi alfahari ga mutane da bautar ubangijinka, idan ka kyauta sai ka godewa Allah, idan kuma ka yi munana sai ka nemi gafarar Allah. Kuma babu wani alheri a duniya sai ga mutane biyu: mutumin da ya yi zunubi yana mai riskarsa da yin tuba, da kuma mutumin da yake gaggawa cikin aikata alheri. kuma aiki ba ya qaranta tare da taqawa, yaya kuwa abin da ake karva zai qaranta?

90. Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa mafi cancantar mutane ga annabawa su ne mafi sanin abin da suka zo da shi, sannan sai ya karanta ayar nan “haqiqa mafi cancantar mutane da ibrahim su ne waxannan da suka bi shi, da wannan annabi da kuma waxannan da suka yi imani, kuma Allah shi ne majivancin muminai…”

Sannan sai Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa masoyin Muhammad (S.A.W) shi ne; wanda ya bi Allah koda kuwa nasabarsa ta nisanta, kuma maqiyin Muhammad (S.A.W) shi ne wanda ya savawa Allah (S.W.T) koda kuwa nasabarsa ta kusanta!

91. Imam Ali (A.S) ya ce: -alokacin ya ji wani mutum daga Haruriyya[4] yana sallar dare, yana karatun kur’ani, sai ya ce: Bacci a kan (bisa) yaqini ya fi salla cikin kokwanto.

92. Imam Ali (A.S) ya ce: ku sanya wa labari hankali idan kuka ji shi hankalin kiyayewa ba hankalin ruwaitowa ba, ku sani haqiqa masu ruwaito ilimi suna dayawa, amma kuma masu kiyayewa (sanya masa hankali) ‘yan kaxan ne.

93. Imam Ali (A.S): -a lokacin ya ji wani mutum yana cewa; “Inna lil-Lahi wa’inna ilaihi raji’un” sai ya ce: Haqiqa faxinmu cewa: “Inna lil-Lahi” furuci ne a kan kawukanmu ga mulkin Allah, kuma faxinmu; “Wa’inna ilaihi raji’un” furunci ne a kan kawukanmu da halaka.

94. Imam Ali (A.S) ya ce: -a lokacin da wasu mutane suka yabe shi a gabansa-: Ya ubangiji kai ne mafi sani da ni daga kaina, kuma ni ne mafi sani da kaina fiye da su, ubangiji ka sanya ni fiye da yadda suke tsammani, ka gafarta mana abin da ba su sani ba.

95. Imam Ali (A.S) ya ce: Ba yadda biyan buqatu zai daidaitu sai da abubuwa uku: da qaranta ta domin ta girmama[5], da kuma neman voye ta domin ta bayyana, da kuma gaggauta ta domin ta yi sannu-sannu.

96. Imam Ali (A.S) ya ce: Da sannu wani zamani zai zo wa mutane da ba a kusantarwa a cikinsa sai annamimi, kuma ba a qayatarwa sai fajiri, kuma ba a raunatarwa sai mai adalci, suna ganin sadaka a matsayin abin biyan bashi, kuma sadar da zumunci a matsayin gori, kuma ibada domin neman fifiko a kan mutane! A lokacin ne sarauta (tafiyar da mulki) zata kasance da shawarar bayi, da jagorancin yara, da kuma tsarawar fixiyayyun mutane!

97. Imam Ali (A.S) ya ce: -yana sanye da wani zane tsoho da ya qoqe, sai aka yi masa magana game da haka. Sai (A.S) ya ce: Zuciya tana tsoratuwa saboda shi, kuma rai tana qasqantuwa da shi, kuma muminai suna koyi da shi.

98. Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa duniya da lahira maqiya ne biyu masu karo da juna, kuma hanyoyi biyu ne masu savawa, duk wanda yake son duniya ya jivance ta to sai ya qi lahira ya yi gaba da ita, su kamar gabas da yamma ne. mai tafiya tsakaninsu duk sadda ya kusanta da xayarsu sai ya yi nesa daga xayar, kuma su masu kishiyantar juna ne!

99. Daga Nuf al’bikaliyyu, ya ce: Na ga Imam Ali (A.S) a wani dare, ya fito waje daga kan daga shimfixarsa, sai ya saurara kaxan sannan sai ya ce: Ya kai Nuf, shin kana bacci ne ko kuma kana farke?

Sai na ce: Ina farke ne ya amirul muminin.

Sai ya ce: Ya kai Nufu, Farin ciki ya tabbata ga masu gudun duniya, masu kwaxayi a lahira, waxannan su ne mutanen da suka riqi qasa mashimfixa, turvayarta kuma shimfixa, ruwanta kuma daddaxa, Kur'ani kuwa alami[6], addu’a kuwa tufafi[7], sannan sai suka yayyaga (kekketa) duniya irin yayyagawar nan (irin ta tafarkin) da Masihu (A.S) (annabi Isa) ya yi mata.

Ya kai Nufu, Haqiqa Dawud (A.S) ya tsaya daidai irin wannan awar ta dare, sai ya ce: wannan sa’a ce da babu wani bawa da zai kira Allah ya yi addu’a a cikinta sai an amsa masa, sai dai idan ya kasance mai karvar haraji ne, ko kuma xan leqen asiri, ko kuma xan sanda, ko mai buga ganga, ko kuma makaxi.

100. Imam Ali (A.S) ya ce: Haqiqa Allah maxaukaki ya farlanta muku wasu farillai to kada ku tozarta ta, kuma ya shata muku iyaka kada ku shige ta, kuma ya hana ku wasu abubuwan to kada ku keta (kutsa) su, sannan ya yi shiru gabarin wasu abubuwa da bai bar su ba don mantuwa, to kada ku xora wa kanku nauyinsu.

Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria
Hfazah@yahoo.com


[1] - Wannan Magana tasa tana daga tausasan zattuttuka da fasaha, ma’anarsa ita ce: mu idan ba a ba mu hakkinmu ba sai mu zama cikin kaskanta, domin wanda aka goya a baya yana hawa kan duwainiyar rakumi ne, kamar bawa da ribatacce, da makamantansu.

[2] - Wato mai hankali baya Magana sai ya shawarci zuciyarsa, tunaninsa ya ba shi umarni, amma wawa furta maganarsa yana rigon tunaninsa, da tace ra’ayinsa.

[3] - Da sara irin na maciji.

[4] Hawarijawa.

[5] Qaranta ta wajen nema, domin ta girmama da biyan buqata, da kuma voye ta domin ta bayyana bayan biyanta. Kuma idan ta yi sannu-sannu sai a ji daxinta.

[6] Alami: da suke karantawa a asirce domin wa’aztuwa da xaukar darussa da tunani a cikin zurfafan ma’anoninsa.

[7] Tufari ne: saboda suna karanta ta a fili domin bayyanar da qasqanta da rusunawa ga Allah (S.W.T).